ABNA24 : Tashar talabijin ta Rusiyal Yau ta kara da cewa motocin sun shiga kasar Siriya ne ta barauniyar kufar shiga kasar mai suna Al-Walid, inda suka nufi cikin kasar.
Labarin ya kara da cewa mai yuwa motocin zasu je Yankunan Dair- Zur da kuma Hasaka inda Amurka take da sansanonin sojojinta.
Kungiyar yan ta’adda ta kurdawan Kasad wacce take samun goyon bayan Amurka ce take taimkawa sojojin kasar na Amurka a irin wadannan ayyuka.
Kafin haka dai sojojin na Amurka wadanda suke mamaye da wasu yankuna a arewa maso gabacin kasar Siriya tun shekara ta 2016 suna satar danyen man fetur a yankin tare da taimakon kungiyar yan tawaye ta kurdawan kasar ta Siriya wacce ake kira Kasad.
342/